Joe Biden Ya Samu Nasara ne Saboda An yi Maguɗi a Zaɓen – Trump

0
312

Shugaban kasar Amurka, Donal Trump ya ce babban mai hamayya da shi a zaben kasar na shekarar 2020, Joe Biden, ya lashe zabe ne saboda an yi murdiya a zaben.

Trump, wanda yaki aminta da shan kayi, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter yau Lahadi.

Sakamakon baya-bayan nan da ya fito ya nuna cewa dan takarar jam’iyyar Democrat Joe Biden ya samu jumillar yawan kuri’un wakilan zabe 306 yayin da Trump yake da 232.

A ranar Juma’a ne dai kafafen yada labarai na kasar Amurka su bayyana cewa Joe Biden ya lashe zabe a jihar Georgia.

Trump ya wallafa cewa, “Ya samu nasara ne saboda anyi murdiya a zaben. Ba abar masu sanya idanu ba,”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here