Ɗalibai Su Fara Shirin Komawa Makarantu Mako Mai Kamawa – ASUU

0
619

Kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa ASUU, ta fadawa Dalibai da su fara shirya komawa makarantu mako mai kamawa.

ASUU ta fadai haka ne a shafinta na Twitter a yayin da kungiyar ta bayyana fatan cimma matsaya tsakaninta da gwamnatin tarayya.

Kungiyar ta bayyana fatan cewa dalibai za su koma jami’a mako mai kamawa bayan tattaunawar da za tayi da gwamnati.

“Duk daliban jami’o’in gwamnatin tarayya su shirya komawa yayin da muke tsammanin sakamako mai kyau daga kungiyar ASUU ranar Laraba”.

Hakan na zuwa ne bayan da ministan kwadago da nagartar aiki, Chris Ngige, a ranar juma’a ya bayyana fatan cewa za’a kammala cimma matsaya da kungiyar mako mai kamawa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here