Ƴan bindiga sun sace mutum 3, sun harbi malami a Kwalejin Fasaha a Zaria

0
216

Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun kai hari kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli dake Zaria.

Rahotanni sun ce, sun harbi Lakcara daya tare da sace ya’yansa guda biyu da kuma wani mutum daya.

Yan bindigar sun kai harin ne a jiya Asabar.

Shugaban sashin koyar da fasahar ilimin na’ura mai kwakwalwa ne yan bindigar suka kaiwa hari, mai suna Injiniya Bello Atiku.

Shima wani Lakcara mai suna Injiniya Abdullahi ya tsallake rijiya da baya sai dai ya samu raunika.

Shugaban makarantar, Injiya Kabir Abdullahi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya yi bayanin cewa ” yan bindigar sun shiga makarantar ne da misalin karfe 9 na daren ranar Asabar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here