Yadda Hadimin Ganduje Ya Gwangwaje Matasan Kano Da Tallafin Jakuna

0
203

Murtala Gwarmai, babban mataimaki na musamman kan ci gaban matasa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya tallafawa matasa da Jakuna.

Gwarmai ya ce matasan ne suka nemi a basu Jakunan don tallafa mu su wajen daukar yashi, marmara da duwatsu wanda hakan zai bunksa kasuwancinsu.

Sauran abubuwan da ya raba sun hada da babura, Kekuna, bulo da rufin daki da sauran su.

An yi rabon kayan tallafi ne a harabar ma’aikatar ci gaban matasa da wasanni inda mutane 40 suka amfana.

Hadimin gwamnan ya ce zai ci gaba da tallafawa matasa.

Kabiru Ado Lakwaya, kwamishinan harkokin matasa da wasanni na daga cikin jami’an gwamnati da suka samu halartar taron rabon kayan tallafin.

Sai dai bullar wannan labari ke da wuya ya ja hankalin al’ummar kasarnan da manyan jaridun kasarnan da ma na Ketare.

Yayin da wasu ke jinjina ga hadimin Gandujen bisa raba tallafin Jakuna a yayin da aka yi karin kudin man fetir, wasu kam na ganin hakan a matsayin abinda bai dace ba ganin cewa ba wani amfani da zaiwa matasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here