Jaruma Yetunda Bakare Ta yi Barazanar Fallasa Mazan Dake Turo mata Hotunan Tsiraici

0
287

Yetunda Bakare, shahararriyar jarumar wasan kwai-kwayo ta yi barazanar fallasa wasu maza da ke turo mata hotunan tsiraici.

Jarumar ta fina-finan Yarabanci ta bayyana hakan ne a kasan hoton da ta wallafa a shafinta na Instagram.

“Ina Rokon ku, gabadaya wadanda suke turo min hotunan tsiraici a manhajar sako, da su dakata da yin hakan kafin na tona asirin ku a bainar jama’a” inji ta.

“Bana damuwa kan tsayin al’aura, don haka ku dakata da bata min rai. Yanzu mutum bazai iya duba manhajar aiko sakonsa cikin lumana ba. Don haka a kiyayeni”.

Bakare dai ba ita ce jaruma ta farko da fara bayyana irin yadda magoya bayanta ke turo mata sakonni irin wannan ba.

A watan Afrilu ma, sai da mawaki, Naira Marley ya roki yan matan dake turo masa hotunan tsiraici da su dena hakan saboda lokacin yana yin Azumi”.

“Zuwa ga masu turo min hotuna da bidiyon tsiraici, su dakata a yanzu. Lokacin da bana Azumi bakwa turo min hotunan tsiraici, don haka yanzu ku dena turo mon”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here