Za’a Sake Buɗe Filayen Jiragen Kano Da Fatakwal Don Zirga-Zirgar Ƙasashen Ƙetare

0
209

Gwamnatin tarayya ta shirya sake bude filayen sauka da tashin jiragen sama na malam Aminu Kano da na Birnin Fatakwal don zirga-zirgar kasashen keatare watanni uku bayan ta bude filin jirgi na Legas da Abuja.

Darakta Janar na hukumar kula da zira-zirgar jirage ta kasa, Musa Nuhu ne ne ya bayyana hakan yayin taron yiwa manema labarai jawabi da kwamitin yaki da Korona na fadar shugaban kasa ke yi a Abuja.

Musa Nubu ya ce za’a bude filayen sauka da tashin jiragen guda biyu ne yayin da aka samar da kayayyakin aiki na zamani da kuma isassun ma’aikata a filayen jiragen.

Malam Nuhu ya ce sake bude filayen jiragen ya zama wajibi don rage cunkos a fikayen jirgin Abuja da Legas da kuma samar da yanayi mai kyau ga matafiya.

Ya kuma kara da cwwa hukumar na jiran gamayyar kungiyoyin dake yaki da anmobar Korona da su samar da kayayyakin aiki na zamai da ake bumata yayinda sashin kula da lafiya na filayen jirgin suke kokarin samar da ma’aikatan da ake bukata.

Haka kuma daraktan janar din bayyana ranar sake bude filayen jirgin ba, sai dai ya ce za’a bude su nan bada jimawa ba.

Idan za’a iya tunawa dai a ranar 5 ga watan Satumba ne gwamnatin tarayya ta sanar da dawowa da zirga-zirgar jiragen kasashen ketare.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here