Kasafin Kuɗi: Gwamnatin Kano Ta Ware Kaso 17 Don Kula da Asibitoci a Masarautun Jihar

0
236

Gwamnatin jahar Kano ta tsara kashe kaso Goma Sha Bakwai cikin Dari na kudirin kasafin kudin shekarar badi wajen kammala aikin daga darajar manyan Asibitoci Hudu dake manyan masarautun jahar kano.

Kwamishinan ma’aikatar lafiya Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bayyana haka ga manema labarai jim kadan da Kare kudurin kasafin kudin ma’aikatar lafiya a majalisar dokokin jahar kano.

Ya bayyana cewa gwamnati za ta cigaba da aikin gina cibiyar yaki da cutar Daji a Asibitin Kwararru na Mohd Buhari dake Giginyu.

Shi ma shugaban hukumar kula da Asibitoci ta jahar kano Dr. Nasir Alhassan Kabo da takwaransa na Hukumar lafiya matakin farko Dr. Tijjani Hussaini da kuma na hukumar Samar da magunguna ya jaha Dr. Isham Imamuddeen da kuma shugabar hukumar kula da Taimakekeniyar Lafiya Dr. Halima Mijin yawa sun kare kasafin kudin ma’aikatunsu a gaban kwamitin kula da lafiya na majalisar.

Shugban kwamitin kuma wakilin Karamar Hukumar Wudil Hon. Nuhu Abdullahi Achika ya ce za su kara yin nazari akan tanadin aiyuka da ma’aikatun suka yi tare da hada cikakken rahoto akai.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here