Kwankwaso Ya Jinjinawa Kungiyar Izala Bisa Kokarinsu Na Bunkasa Ilimi

0
155

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yabawa kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunnah bisa bada muhimmanci ga fannin ilimi.

Sanata Kwankwaso ya yi yabon ne yayin da ya ziyarci Shelkwatar kungiyar dake Abuja don yin ta’aziyya ga Sheikh Kabiru Haruna Gombe bisa rasuwar mahaifiyarsa.

Kwankwaso ya ce ya lura da yadda kungiyar Izala ta ke kokari wajen ilimintar da al’umma ta hanyar kafa jami’ar kasa da kasa a garin Hadejia dake Jigawa.

Ya kuma kara da cewa, Izala na wayar da kan al’umma ta hanyar kafa tashar MANARA.

Tsohon gwamnan na Kano, ya ce ya so ziyartar jihar Gombe don yin ta’aziyar amma ba samu dama ba.

Kwankwaso ya yi addu’ar, Allah ya jikanta ya sa aljanna makoma.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here