Kasafin Kuɗi: Gwamnatin Kano Za ta Kashe Bliyan 11 Don Kammala Aikin Tituna a Jihar

0
228

 

Kwamitin majalisar dokokin jahar kano mai kula da harkokin matasa da wasanni da na Ayyuka da kuma na ilimi mai zurfi sun karbi shugabannin ma’aikatun gwamnati da suka zo Kare kudirin kasafin kudinsu na shekarar 2021.

Shugaban kwamitin Matasa da Wasanni Hon. Nuraddeen Ahmad Alhassan wakilin Karamar Hukumar Rano da wakili a kwamitin Kula da Aiyuka Hon.Comrade Musa Ali Kachako wakilin karamar hukumar Takai da kuma takwaransa na kwamtin Ilimi mai zurfi Hon.Nuhu Abdullahi Achika wakilin Karamar Hukumar Wudil sun nuna gamsuwarsu akan tanadin muhimman aiyuka da ma’aikatun suka yi a kudirin kasafin kudinsu na shekarar mai zuwa kamar yadda yake a sanarwa da sakataran yada labarai na majalisar
Nura Bala Ajingi ya fitar.

Kwamishinan ma’aikatar Ayyuka Alh. Idris Garba Unguwar Rimi ya ce an kiyasta kashe Naira Biliyan 11.8 domin kammala dukkanin aikin Tituna masu tsawon kilomita Biyar da ci gaba da sauran aikin gina Tituna a sassa daban daban da kuma cibiyar yaki da cutar Daji a Asibitin Mohd Buhari dake Giginyu.

Shi kuwa babban sakatare a ma’aikatar Matasa da wasanni Alh. Ibrahim Ahmad Sagagi ya ce kasafin kudin zai mayar da hankali wajen bunkasa Cibiyoyin wasanni a masarautu Hudu da horar da matasa harkokin dogaro da kai.

Da take jawabi ga manema labarai bayan kare kasafin kudin shugabar ma’aikata Hajiya Binta Ahmad Lawan ta ce gwamnati ta tsara daukar Karin ma’ikata Dubu 5 da horar da wadanda suke aiki a shekarar 2021.

Sauran hukumomin da suka kare kasafin kudin sun hada da Hukumar Tace Fina finai da Dab’i da kuma Jami’ar Yusuf Maitama Sule.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here