Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano Za ta Fara Sanya Idanu Kan Fina-Finan Hausa a Shafin YouTube

0
151

Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano ta ce ta shirya fara lura da shafukan fina-finan Hausa na YouTube don hana haska abubuwan da basu dace ba.

Babban sakatare a hukumar, Isma’il Na’abba, ne ya bayyana hakan yau Alhamis a Kano yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasa wato NAN.

“A bisa manufofin wannan hukuma, mun gayyaci masu amfani da shafun YouTube, wadanda suke dora fina-finai don samar da fahimtar juna.

” Yana daga cikin karfin wannan hukuma ta kula tare da tace duk wani na’u’in fim wanda yake na sauti, wanda ake gani ko a rubuce, wanda kuma aka yi shi don mutane.

“Mun yi musu bayanin cewa, kowanne dole ne ya kawo fim dinsa wannan hukumar don tantancewa kafin ya dora a wadannan shafuka”, inji shi.

Na’abba, wanda ya yi gargadin cewa hukumar za ta hukunta duk wanda ya kaucewa umarnin ya bukace su da su dinga tuntubar hukumar domin neman shawara da karin bayani.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here