Gwamnatin Kano Na Shirin Bada Tallafin Karatu Ga Ɗalibai Dubu 60 Ƴan Asalin Jihar

0
267

Babban Sakatare na hukumar bada tallafin karatu ta jihar Kano, Alhaji Abubakar Zakari, ya ce daliban jihar Kano dubu 60 ne za su amfana da tallafin karatu na shekarar 2020.

Ya shaidawa kamfanin dillancin labarai a ranar Talata cewa, sama da dalibai dubu 50 ne suka nemi tallafin zuwa yanzu.

Abubakar Zakari ya ce, hukumar tunda farko ta samaar sa form dubu 40 ga dalibai don su nemi tallafin wanda aka fara tun 1 ga watan Satumba, inda ya kara da cewa an kara shi zuwa dubu 60.

Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar ta kara yawan alawus din da ake ba wa dalibai na tallafin da suke karatu a manyan makarantu.

Ya ce gwamnatin jihar Kano ta ware kudi Naira Biliyan 1.8 don biyan tallafin karatun ga dalibai yan asalin jihar Kano.

Ya kuma ce an ware Naira Miliyan 700 don biyan tallafin karatu ga daliban da suke makarantu masu zaman kansu a fadin kasarnan.

Babban Sakataren ya kuma bayyana cewa, an ware miliyan 247 don biyan tallafin karatu ga dalibai yan asalin jihar Kano dake Karatu a makarantar koyar shari’a ta Najeriya.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here