EFCC Na Neman Wanda Ya Shigo Da Tsarin InskNation Ruwa a Jallo Bisa Zarginsa Da yin Damfara

0
1049

Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta ayyana Omotade-Sparks Amos Sewanu wanda ya shigo da tsarin InksNation a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin damfarar kudi ta Naira miliyan 32 a yayin da ya shigo da tsarin fitar da kudi ta kafar sadarwa da ake kira “Pinkoin”.

Hukumar ta EFCC, a wani talla da ta wallafa a jaridar The Nation a yau Laraba, ta kuma zargi Sewanu da samun kudi ta haramtacciyar hanya.

Mista Sewanu ya na ikirarin zai kawar da talauci a Najeriya cikin wata 6 ta hanyar ba wa kowanne dan kasa Naira dubu 120, 000 kowanne wata a tsarin InksNation wanda aka fara a shekarar 2019.

A wata wasika da ya rubutawa hukumar EFCC, ya yi bayanin cewa har jinjiraye sabbin haihuwa da ake haifa a kullum za su samu kudi Naira 120, 000 kullum idan aka amince da tsarin.

Ya kuma yi bayani sosai a shafin InksNatio na twitter inda ya yi ikirarin cewa, idan kudurinsa ya gaza a kasa da shekara daya, a kai shi gidan kaso har na tsawon rayuwarsa.

A watan Yuni, masu ruwa da tsaki na Blockchain Technology Association of Nigeria (SIBAN) sun bayyana tsarin Pinkoin na InskNation a matsayin damfara.

SIBAN sun yi gargadin cewa, “al’umma su kiyayi tsarin InksNationa.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here