Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Hukumar Zaɓe Ta KANSIEC Ta Nemi Haɗin Kan Ƴan Jarida

0
215

Daga Nusaiba Abdul’aziz Muhammad

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano(KANSIEC), Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya hori yan Jarida a jihar da su yi amfani da kwarewar su wajen taimakawa hukumar don gudanar da aikinta.

Farfesa Sheka na fadin hakan ne yayin da yake karbar shugabannin kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Kano wato Nigerian Union of Journalists, Correspondents Chapel wadanda suka kai masa ziyara a ofishinsa.

Ya ce yan kungiyar an san su wajen wayar da kan al’umma kan manufofi da tsare-tsaren gwamnati a dukkan matakai inda ya bukace su da su dore a kan hakan.

“Rawar da kuke takawa a wajen ilimantarwa da wayar da kan al’umma bazai misaltu ba. Akwai bukatar ku rubanya kuma ku sanar da al’umma abubuwan da yakamata ayi da wanda bai dace ayi ba a yayin zabe”, inji shi.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar ta wakilan kafafen yada labarai ta Kano, Alhaji Ibrahim Garba ya ce sun ziyarce hukumar ne don karfafa alakar dake tsakani da kuma tattauna hanyoyin yin aiki tare don cimma muradin da ake fata.

Alhaji Ibrahim Garba ya bayyana cewa, kungiyar na shirin bada horo ga yan jarida daga sauran kafafen yada labarai kan yadda ake bayar da rahota yayin gudanar da zabe.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here