Ina Fatan Mace Ta Zama Shugabar Kasa a Shekarar 2023 – Amina Mohammed

0
166

Mataimakiyar babban Sakataren Majalisar dinkin duniya, Amina Mohammed ta bukaci mata da su karbi mulki daga hannun shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

Amina Mohammed, wacce ke jagorantar tawagar majalisar dinkin duniya a ziyarar da suka kawo Najeriya, ta bayyana hakan ne a wani shirin Talabijin a Abuja.

Tun a ranar Litinin ne dai babbar jami’ar majalisar dinkin duniyar ta tattauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja kan tsare-tsaren tayar da komada bayan illar da annobar Korona ta yi.

Yayin da take jawabi a ranar Talata, Amina Mohammed ta ce dole dukkan yan Najeriya su hada kai don sake gina kasa ba tare da la’akari da kabila ko banbancin ra’ayi na siyasa ba.

Yayin da aka tambaye ta shin ta na muradin mace ta gaji shugaba Buhari a matsayin shugaban Najeriya, sai ta ce ” Wannan shi ne fatana kuma bana ganin cewa akwai macen da baza ta iya hakan ba.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here