Gwamnatin Lagos Za Ta Hana Tinubu Kudinsa Na Fansho

0
214

 

Gwamnatin jihar Lagos ta bayyana aniyarta ta sake fasalin dokar fansho wadda za ta soke kudin fanshon da ake bai wa tsoffin gwamnoni da mataimakansu da suka yi wa jihar hidima, cikinsu har da jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu da kuma Ministan Ayyuka, Babatunde Raji Fashola.

 

Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya bayyana haka a zauren Majalisar Dokoki lokacin da yake gabatar da kasafin kudin shekarar 2021.

Sanwo-Olu ya ce nan gaba kadan zai gabatar da kudirin dokar ga majalisar domin amincewa da ita da zummar rage nauyin da ke wuyan gwamnati na biyan makudan kudade ga ‘yan siyasa a matsayin fansho.

Biyan fansho ga gwamnoni da mataimakansu na daya daga cikin hanyoyin da jihohi ke asarar tarin kudaden da suka dace a yi wa talakawa aiki da su kamar yadda sashin Hausa na  RFI ya rawaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here