An Kama Boka Ya na Lalata Da Matar Aure a Jihar Katsina

0
371

Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Katsina ta kama wani Boka da ya mallake zuciyar wata mata inda suke aikata lalata har zuwa lokacin da ta matar ta gayyaci Bokan zuwa gidanta inda mijin matar ya kama su kan gadonsu na aure.

SP Gambo Isa Jami’an Hulda da jama’a na rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Katsina ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce bokan ya na bawa mata maganin mallakar miji, sannan ya mallake matar tare da yin lalata da ita.

Shima Bokon mai suna Labaras Mujittapha mai shekaru 24 ya bayyana cewa ya bai wa matar ‘taimako sosai’ wajen mijinta da ya’yanta, sannan ya tabbatar da cewa ya sadu da ita.

Sai dai ya musanta cewa shi ya neme ta.

Ita matar mai suna Malam Saratu ta ce, ita fa maganin mallakar miji taje nema wajen Boko, daga karshe reshe ya juye da mujiya.

Sai dai matar ta tabbatar da cewa ita ta nemi Bokan da lalata kuma har abinci take dafawa ta kai masa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here