Kotu Ta Yanke Hukuncin Ɗaurin Rai da Rai Ga Masu Ɗaukar Nauyin Boko Haram

0
307

Kotun ɗaukaka kara ta Abu Dhabi ta samu wasu yan Najeriyu su 6 da laifin daukar Nauyin kungiyar Boko Haram kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya bayyana.

Kamar yadda rahotan ya bayyana, biyu daga cikin waɗanda aka samu da laifin masu suna, Surajo Abubakar da Sale Yusuf an yanke musu daurin rai da rai yayin da ragowar hudun, Ibrahim Ali Alhassan , AbdurRahman Ado Musa, Bashir Ali Yusuf da Muhammad Ibrahim Isa aka yanke musu daurin shekaru 10 a gidan kaso.

Hukuncin kotun ya nuna cewa tsakanin shekarar 2015 da 2016, masu laifin sun aika kudade daban daban wanda ake zargin na tallafawa Boko Haram ne da yawan su ya kai USD782, 000.00 Duk da makusantansu sun ce fitar da kudin anyi shi ne bisa dalilai na gaskiya.

Wannan shi ne karo na farko da aka samu masu daukar nauyin Boko Haram daga wajen Najeriya.

Wani babban jami’in gwamnati ya tabbatar da cewa suna da labari a kan batun.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here