Dan Majalisar Tarayya Ya Gwangwaje Daruruwan Matasa Da Babura Da Keke-Napep A Zamfara

0
156

Dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gusau da Tsafe a majalisar wakilai ta kasa, Hon. Kabiru Amadu Mai-Palace a ranar Asabar ya raba babura masu kafa uku guda 80 da babura masu kafa biyu guda 100 a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Hakan na cikin wani bangare na samar da aikin yi ga matasan dake mazabarsa a jihar, da kuma gudunmawa wajen kawo karshen kalubalen tsaro da talauci tsakanin al’umma.

Jaridar PRIME TIME NEWS ta rawaito cewa, dan majalisar a kwanan nan ya ya ba wa daruruwan matasa jari a jihar da kayayyakin sana’o’i da kudade.

Hakanan na zuwa ne kari kan gine-gine da gyara magudanun ruwa, gadajoji gami da makarantu da sauran su.

Sannan Mai-Palace ya shirya taron tattaunawa da al’ummarsa, da kuma samar da injin markade guda 500 da keken dinki guda 100 ga mata da maza a jihar, ” inji shi.

 

Mai-Palace wanda ya zanta da jaridar PRIME TIME NEWS a ranar Asabar jim kadan bayan kaddamar da shirin raban tallafin , ya bayyana cewa matsalar tsaro a jihar za’a magance ta ta hanyar samar da aikin yi ga mata da matasa da kuma daukar nauyin wasu zuwa makarantu.

“Wannan ya na daga cikin bangare na alkawarurrukan da nayi yayin yakin neman zabe ga yan mazabata sannan tun sanda na shiga ofis ba wani abu na cikan al’umma da ban kula da shi ba, a batun fannin lafiya, ilimi, samar da aikin yi, shirye-shiryen gwmnatin tarayya, rijiyar burtsatsai, siyan abubuwan zama ga makarantu, kujeru ga makarantu kuma bazan iya irga adadin motoci da babura da na rabaw al’ummar yankin nan ba”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here