An Buƙaci Musulmai da Su Ƙauracewa Shafin Muneerat Abdulsalam Da Sadiya Haruna Bisa Zargin Yaɗa Kalaman Batsa

0
974

Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba

Wasu masu kishin kasa ta zauna lafiya da Kuma fafutukar ci gaban addinin Musulunci sun bukaci al’ummar musulmin kasarnan su kauracewa duk wata Haja da Munirat Abdussalam take sayarwa dama Duk wasu shawarwari da ta ke bayar wa a shafinta na YouTube.

Shugaban kungiyar a Kalaba jahar Kuros Riba Alhaji Auwal Muhammad Musa ne ya bukaci haka zantawarsa da ‘Yan jarida a Kalaba.

Yace ” matsayin mu na musulmi Kuma masu waccan fafutuka muna Kira ga al’ummar musulmin Najeriya dama na Duniya baki daya a kauracewa shafin Munirat Abdussalam da Kuma bayanan ta saboda kalamai na fitsara da badala da take yadawa”.

Hakan a cewar su ya saba ka’idar addinin Musulunci kazalika kungiyar har wayau ta nemi sha’iran kano da kewaye su daina Bari sadiya Haruna na fakewa “Tanayin wakokin begen fiyayyen halitta Tana cin zarafin addini itama.

Sun bukaci a Rika hukunta Duk masu Hali da Dabi’a irin tasu domin na fuskar musulunci suke da ita ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here