An Kama Masu Tallan Magananin Gargajiya da Kalaman ‘Batsa’ a Kano

0
197

Daga Nusaiba Abdul’aziz Muhammad

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kama masu sayar da maganin gargajiya 13 da ke amfani da kalaman ‘batsa’ wajen tallata hajarsu.

Babban Sakatare a hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu ta jihar Kano Dr Usman Tijjani Aliyu ne ya sanar da hakan ga manema labarai.

Dr Usman ya Kara da cewa galibin su an kama su a masallatan juma’a ne da suka hadar da na Alfurqan da na Fagge sai na Sharada da kuma Ja’en.

Ya kuma ce sauran an kama su ne a kan manyan hanyoyi da suka hadar da sabon titi zuwa Madobi sai unguwar Guringawa, da kuma titin zuwa gidan zoo.

Shugaba ya ce manufar kama wadannan mutane shi ne a tsaftace sana’ar ta su don su daina amfani da kalaman batsa wajen tallata hajarsu.

Ya kuma ce gwamnati ta kafa kwamitin kartakwana da zai dinga kama masu tallan maganin gargajiya da ke amfani da kalaman da basu kamata ba .

Kwamitin da Gwamanatin ta kafa ya kunshi kwamishinan lafiya na jihar Kano Aminu Ibrahim Tsanyawa a matsayin shugaba, sai kuma wakilai daga hukumomin KAROTA da HISBA, sai kuma rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here