Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Za mu Koma Wayar Da Kai ta Kafafen Yaɗa Labarai -KANSIEC

0
195

Daga Nusaiba Abdul’aziz Muhammad

Bayan kammala wayar da kai a masarautu biyar dake jihar Kano, a shirye-shiryen zaben kananan hukumomi na shekarar 2021, hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano(KANSIEC) za ta yi amfani da kafafen yada labarai don wayar da kan al’umma.

Shugaban hukumar, Farfesa Garba Ibrahim Sheka ne ya bayyana hakan yayin jawabi ga masu ruwa da tsaki a taron wayar da kai na kwana daya a masarautar Rano.

A sanarwar da jami’in hulda da jama’a na hukumar ta KANSIEC, Dahiru Lawan Kofar Wambai ya fitar ta rawaito shugaban hukumar na cewa:

“Bayan zagaye zuwa masarautu biyar, yanzu za mu mayar da hankali zuwa kafafen yada labarai musamman Rediyo Talabijin don ci gaba da wayar da kan al’umma kan yadda za’a gudanar da zaben”.

Shugaban hukumar ya kara da cewa, a halin yanzu akwai Form din takara ga dukkan yan takara bayan jami’iyyun su sun mika sunayen su.

A madadin shugabannin kananan hukumomi goma da ke masarautar, shugaban Karamar hukumar Rano, Alhaji Ya’u Abdullahi Gidan Zangi ya bayyana kwarin gwiwa kan hukumar zaben a muradinta na gudanar da sahihin zabe.

Gidan Zangi ya yabawa gwamnan jihar ta Kano bisa yadda yake gudanar da zaben kananan hukumomi a kan lokaci.

Sarkin Rano, Alhaji Muhammad Kabiru Inuwa ya godewa hukumar bisa ziyarar da ta kai masa tare da addu’ar samun nasarar hukumar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here