Wata Mata a Kano Ta Kai Ƙarar Kamfanin Mudatex Bisa Zargin Amfani da Hoton Ƴarta Wajen Yin Talla

0
205

Wata mata mai suna Hajiya Habiba Aliyu, ta shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, inda ta ke neman kamfanin siyar da tufafi da wasu mutum biyar da su biya diyyar Miliyan dari biyu da hamsin bisa zargin yin amfani da hoton ƴarta wacce ta rasu mai suna Nafisa Aliyu wajen yin tallata.

Habiba ta yi ikirarin cewa, kamfanin ya yi amfani da hoton ƴar ta ba tare da neman izini ba.

Ta yi zargin cewa, wadanda take karar sun kwafi aikin zanen ƴarta a shafin Facebook tare da amfani da shi don jawo hankalin kwastomomi.

Habibia, wacce ta shigar da karar ta hanyar lauyanta, Aliyu Suleiman-Jatau, ta yi ikirarin cewa kayayyakin kamfanin Mudatex da aka siyar tare da zanen hoton yar ta da ta rasu ya tauye mata hakkinta.

Sauran wadanda ake karar sun hada da dan kasar China, Ms Ling Haiying; kamfanin Hongkon Runda Textile, Mudatex Brothers, Dan Kano da Sani Tahir.

Mai shari’a, Justice Sa’adaru Ibrahim-Mark, ta dage zaman kotun zuwa 11 ga Disamba don sauraran karar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here