Hukumar Zaɓe Ta Kano KANSIEC Za ta Ƙarfafa Gwiwar Masu Buƙata ta Musamman

0
260

Daga Nusaiba Abdul’aziz Muhammad

Shugaban Hukumar Zabe mai Zaman kanta ta Jihar kano KANSIEC,  Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce Hukumarsa Za ta yi duk mai Yuwuwa wajen Ganin ta Bai wa Masu Bukata Ta musamman Kwarin Gwiwa ta Hanyar Fitowa Takara a Zaben Shugabanin Kananan Hukumomi da ke Tun Karowa.

Shugaban ya Bayyana Hakane sa’ilin da Kungiyar Masu Bakata ta Musamman a Bangaren Gani suka kai ziyara ta Musamman offishinsa.

Da yake Jawabin Farfesa Garba Sheka ya sa ke Jadda mus u cewa Ko shakka Babu Hukumar za ta yi duk mai yuwawa ta hanyar mika Form din takara ga duk wani mai bukata ta musamman da zarar ance Jam’iyyarsa ta tsaidashi a matsayin wanda zai tsaya mata.

Shima a nasa Bangaren Shugaban Kunyar Masu Bukata ta Musamman a Fannin Ganin Abdulhamid Muhammad Sulaiman dakata yace Yazama Wajibi Su yabawa Kokarin da Hukumar Zaben keyi Musamman a fannin Bai wa Kowa Dama tun daga Masu Bukata ta Musamman har  izuwa lafiyayyu.

A karshe Daukacin yan Kungiyar sun nemi da a debi wasu daga cikinsu Aikin Zaben Cikin Ma’aikatan da Hukumar zata Dauka guda Dubu 48 Domin su bayyana irin tasu Basirar.A

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here