Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Sarkin Bichi Ya yi Kira Da’a gudanar da Sahihin Zaɓe

0
247

Daga Nusaiba Abdul’aziz Muhammad

Mai martaba sarkin Bichi Alh Nasiru Ado Bayero ya ja hankalin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, dangane da tabbatar da anyi zabe mai cike da gaskiya da adalci a zaben shugabannin kananan hukumomi jihar dake tafe watan junairun shekarar 2021.

Alh Nasiru Ado Bayero yayi wannan jan hankalin ne yayin ziyarar da hukumar ta KANSIEC ta kai masa a fadar sa, a wani bangare na shirye shiryen taron wuni guda na masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 9 dake karkashin masarautar, musamman dangane da zaben da hukumar su zata gudanar a ranar 16 ga watan junairun sabuwar shekara.

Mai martaba sarkin na Bichi ya kuma bukaci yan siyasa kan su kaucewa tsarin siyasar nan na a mutu ko ai rai, tare da rungumar kaddamar a lokacin da aka sanar basu samu nasara, kuma su tabbata sun marawa wanda yayi nasara baya domin cigaban yankin.

Da yake maida jawabi shugaban hukumar zaben mai zaman kanta ta jihar Kano , Professor Garba Ibrahim Sheka, ya bayyana cewa sun je masarautar ne domin neman albarka, tare da bayyana mata irin shirye shiryen da suka yi dangane da zaben shugabannin kananan huikumomi mai zuwa.

A jawaban su daban daban a yayin taron shugaban karamar hukumar Bichi da takwaransa na Dambatta sun ce zasu cigaba da wayar da kan jama’ar su muhimmancin da zaman lafiya ked a shi a kafin, lokacin, da kuma bayan zabe.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here