Gwamnonin Najeriya Za Su Tattauna Kan Yanayin Tsaro a Yau Laraba

0
95

Gwamnonin jihohi 36 za su gudanar da taro yau Laraba, kan lamuran tsaron kasa da kuma halin da ake ciki kan rushe rundunar SARS, wacce ayyukanta a wasu sassan kasarnan su ka jawo zanga-zanga.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa mai taken ‘Taron gwamnoni Najeriya karo na 21 ta kafar sadarwa’, kuma mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na kungiyar, Abdulrazaque Bello-Barkindo.

Ya yi bayanin cewa, gwamnonin za su kuma yi duba kan fara raba tallafin rage radadin Korona da kungiyar CACOVID ta bayar da kuma yadda aka fasa rumbunan ajiye kayan tallafin bayan zanga-zanga.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here