Ba’a Taɓa Shugaban Da Ya yaƙi Talauci Irin Buhari Ba – Lai Muhammad

0
189

 

Ministan yaɗa labarai na Najeriya Lai Muhammad, ya ce ba a taɓa yin wani shugaba a tarihin Najeriya da ya ƙirƙiro da shirye-shiryen yaƙi da talauci a ƙasar kamar shugaba Muhamadu Buhari ba.

Jaridar Vanguard ta ambato ministan na bayyana haka, yayin wani taron gwamnonin arewacin Najeriya da ya gudana a jihar Kaduna.

Lai Muhammad ya ce shirye-shiryen sun maida hankali wajen taimakawa matasa kai tsaye, da kuma kawar da talauci a tsakanin mata da da waɗanda ke cikin gararin rayuwa.

An gudanar da taron ne ƙarkashin jagorancin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, da wanda shine mai masaukin baƙi.

Taron ya kuma samu halartar wasu jagororin arewacin Najeriya, ciki har da sarakuna da sauran masu fada a ji kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here