‘Mun Samar da Form Din Takara Kyauta Ga Masu Bukata Ta Musamman’ – KANSIEC

0
82

Daga Nusaiba Abdul’aziz Muhammad

Shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC),  Farfesa Garba Ibrahim Sheka,  Ya ce Ya zuwa Wannan Lokaci Hukumarsa Ta samar da Takaddar Shiga Takarar Zaben Shugabanin Kananan Hukumomi da Kansiloli kyauta ga Masu Bukata ta Musamman Domin Basu damar Wakiltar Al’umma.

Shugaban Ya bayyana Hakane Biyo bayan Kiraye-Kirayen da Masu Bukata ta Musamman sukayi na neman Basu Damar Gwada nasu wakilcin ga Al’ummar Jihar ta Kano.

A karshe Farfesa Sheka ya Bayyana Cewa Duk Dan Takarar dake da Lafiya mace ko na miji ya zama Wajibi ta mallaki Form din a kudi Naira Dubu Dari biyu da Hamsin a Matsayin na Shugaban Karamar Hukuma yayin da Dan Takarar Kansila Zai iya Mallakar nashi a Naira Dubu Dari da Hamsin.

A karshe Shugaban ya ce Hukumar za ta dibi Ma’aikatan da za su yi aikin Zaben a Ranar 7 ga watan December na Shekarar 2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here