Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano KANSIEC Ta Yi Gargaɗi Ga Ƴan Takara

0
225

Daga Nusaiba Abdul’aziz Muhammad

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Jihar Kano(KANSIEC) ta ja Hankalin ‘yan Takarar Shugabannin Kanan Hukumomin Fagge, Gwale,municipal, ungogo,Nasarawa,Dala da kuma Kumbotso Dasu kansace masu Biyayya Hadi da Fadin Gaskiya ga Al’umma Yayin Da Ake Gudanar da Zaben kanan Hukumomin dake Karatowa.

Shugaban Hukumar zabe ta Jihar Kano Farfesa Garba Ibrahim Sheka,  Shi ne ya Bayyana Hakan a Taron da Hukumar ta Shiryawa Ciyamomin dake kan Kujerunsu a Babban Dakin Taro dake Karamar Hukumar Ungogo.

Farfesa Garba,  ya Kara da cewa Hukumar sa Shirye ta ke tsab wajen ganin ta Hukunta Duk wani Dan Takara dake da aniyar tada tarzoma a yayin gudanar da zaben kanan hukumomin.

Kazalika Farfesan,  ya ce ya zuwa wannan lokaci hukumar ta Kudiri Aniyar zagaye zuwa Kafatanin Kanan Hukumomi 44 dake Fadin Jihar Domin Fadakar da Duk Wani Dan Takarar Kujerar Shugaban Karamar Hukama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here