Gwamnatin Kano Ta Yabawa Al’ummar Jihar Bisa Kokarin Bin Dokar Tsaftar Muhalli Ta Karshen Wata

0
115

 

Daga Nusaiba Abdul’aziz Muhammad

Gwamanatin Jihar Kano ta ce Yazuwa wannan Lokaci Al’ummar Jihar na Kokari wajen Ganin Sun bi Dokar Takaita Fita a yayin da Ake Gudanar da Zagayen Duba Gari wanda ake Gudanarwa a Duk Asabar din Karshen Wata.

Bayanin Hakan ya fitone ta Bakin Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano,  Dr. Kabiru Ibrahim Getso yayin da Ya kai Ziyarar gani da Ido zuwa Unguwar Kurna Inda yace ko shakka Babu yazama Wajibi Gwamnatin Jihar ya Yabawa Kokarinsu na Bin Doka da Oda.

Jaridar PRIME TIME NEWS ta Rawaito Cewa Getso ya kara Da cewa adai zagayen duba garin ansamu nasarar dakume wata Mota Makare da Kayan Masarufi musamman Fannin Irinsu Madara da Sauransu wanda basu da Shaidar Ingancin Abinci Ta NAFDAC.

A karshe Kwamishinan ya gargadi masu Baburin Adaidaita,  dasu kasance masu Biyayaya ta Hanyar Bin Dokar zaman gida Domin Gudanar da Tsabtar Muhallin Da Aka saba A Duk Karshen Wata a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here