Gwamnan Jihar Imo Ya Nemi Afuwar ‘Yan Arewacin Kasarnan

0
193

Daga Musa Muhamad Kutama, Kalaba

Gwamnan Jihar Imo,  Hope Uzodinma ya nemi afuwar al’ummar Arewacin kasar Nan da suyi hakuri su ci gaba da aike musu da kayan abinci zuwa Jahohin kudu maso Gabas lura da cewa kayan abinci Duk da suke amfani dashi yawanci daga Arewa ake kawo musu shi yankin.

Ire-iren kayan abinci da Dabbobi da ake kaiwa kudu maso Gabas da suka yanke sakamakon kisa da kona dukiyoyi da kadarori da matasan yankin sukayi na milyoyin Naira sun hada da Wake, Albasa ,shinkafa da Kuma Dabbobi Awaki da shanu.

Tun daga lokacin da masu zanga-zangar Endsars suka farwa mazauna Jahohin Abiya, Ribas da Imo kungiyar masu sana’ar kayan lambu da ta motocin sufuri suka yanke shawarar daina Kai kayan kasuwa yankin kudu maso Gabas.

Gwamnan Jahar Imo Hope Uzodinma ya tashi mataimakimsa na musamman kan harkokin jama’a Garkuwa Hausawan Imo Alhaji Suleman Ibrahim Suleman ya jagoranci mutane su tafi Arewa zuwa Kaduna su lallashi Yan kasuwa su kawo musu kayan abinci zuwa jahar Imo.

Bayan da suka dawo daga balaguron Alhaji Suleman Ibrahim Suleman Garkuwan Hausawan Imo ya ce,  “Tabbas Gaskiya ne ni na jagoranci mutum 16 muka tafi Kaduna Gwamna ya turani da a lallashi mutanen mu abasu hakuri su gaba da kawo kayan abinci jahar Imo tunda mu nan lafiya kalau ake Babu wata fitina ko hatsaniya da akayi”injishi.

Mataimakin na musamman kan alamuran jama’a Alhaji Ibrahim Suleman Garkuwan Hausawan Imo yaci gaba da cewa “Munje Babbar kasuwar Kaduna wato central da Kuma Zariya Kan hanyar kano kasuwar Albasa mun lallashi mutanen mun Basu hakuri sun huce sun yarda zanaccen nan da nakeyi da kai kaya ma yafi 1000 da aka kawo mana nan Imo anci gaba da Hulda ta kasuwanci tsakanin mu Babu matsala”.

Yace kungiyar ta tabbatar Masa cewa “Jihar Abiya (Aba) ne da Ribas (Fatakwal ba zasu kai kaya ba” Al’ummar Hausawa mazauna jihar Imo sun jinjinawa gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma da mataimaki na musamman kan harkokin jama’a Suleman Ibrahim Suleman bisa jajircewa taimakawa Al’ummar Hausawa mazauna jahar Imo da sukeyi.

A Imo mafi kankantar Albasa kwara daya ana sayar da ita naira 500 buhunta Kuma dubu 70.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here