Jami’ar Bayero Kano Ta Karrama Dr. Hajara ta Sashin Koyar Da Aikin Jarida

0
182

Jami’ar Bayero ta gabatar da shaidar karramawa ga Dr. Hajara Umar Sanda ta sashin koyar da aikin Jarida na Jami’ar bisa aiki tukuru da sadaukarwa yayin da take a matsayin mataimakiyar shugaban sashin kula da harkokin dalibai.

Hakan na dauke ne cikin wata wasikar yabawa mai dauke da sa hannun mataimakiyar magatakardar sashin kula da harkokin dalibai, Malam Anisatu Uwai Muhammad.

Wasikar ta kara da cewa, sashin kula da harkokin dalibai na jami’ar bayero ya jinjinawa Dr. Hajara Bisa himmarta, Sadaukarwa gami da aiki tukuru wajen ci gaban sashin.

Yayin da yake gabatar da wasikar ta yabawa ga Dr. Hajara, shugaban jami’ar Bayero Kano, Farfesa Sagir Adamu Abbas ya taya ta Murna tare da nuni da cewa karramawar ani ta ne bisa kokarin ta da gudunmawar da take badawa don ci gaban sashin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here