Buhari Ya Umarci Ministoci Da Su Mika Rahotan Abinda Ya Haifar Da Zanga-Zangar EndSARS a Jihohin Su

0
96

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministocin sa da su gabatar da rahotan tattaunawar da suka yi da al’umma a jihohin su kan zanga-zanagr EndSARS mako mai zuwa.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a shirin gidan talabijin na Channel, sannan ya kara da cewa wasu daga cikin ministocin har yanzu basu kammala tataunawa a jihohin su ba.

Mista Femi Adesina yayi bayanin cewa rahotan da ministocin za su gabatar zai ba wa gwamnatin dama wajen gano dalilan da su haddasa zanga-zangar EndSArS.

A gefu guda kuma kuma fadar shugaban kasar ta soki kungiyar kare hakkin dan’adam ta amnesty international bisa fitar da abinda yake ba dai-dai ba kan abinda ya faru a Lekki Toll gate ranar Talata 20 ga watan Oktoba.

Femi Adesina ne ya bayyana hakan inda ya kara da cewa harbe-harben da ya faru a Lekki bai kai ga yin muni ba kamar yadda kungiyar kare hakkin dan’ adam ta yi ikarari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here