Gwamnan Imo Ya Ba da Tallafi Ga Hausawan Da Zanga-Zangar EndSARS ta Shafa a Jihar

0
152

Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba

Gwamnan Jihar Imo,  Hope Uzodinma ya bai wa iyalan Wadanda masu zanga-zangar Endsars suka kai musu farmaki kyautar kudi Naira dubu 500 su ci abinci sakamakon Mijin su da zauna gari banza suka kashe a zanga-zangar Endsars a kasuwar Albasa ta orlu jihar Imo.

Da yake tabbatar da hakan,  Alhaji Suleman Ibrahim Suleman kanin sarkin Hausawan Owerri,  yace “Gwamna ya bai wa iyalan mamaci na biyu da aka kashe dubu dari biyar suci abinci”.

Yaci gaba da bayani yana cewa “mutum biyu kadai aka kashe daya mutum na farko harbinsa sukayi masu zanga-zangar,  aka kaishi asibiti shi Kuma na biyu direba ne,  Wake ya kawo “suka daka Masa wasoso suna dibar waken a mota Sai yace musu su Bari ya Isa haka Sai ya shiga motar zai ja ya tafi Sai Wani cikin masu zanga-zangar ya cire Bindiga ya harbe shi ya mutu nan take”injishi.

Dangane da mamatan biyu Alhaji Suleman Ibrahim kanen sarkin Hausawan Owerri ya bayar da Haske kamar haka ” mutum biyu ne aka kashe na farko ban Sani ba ko yana da iyali na biyu Kuma direba ne shi ya kawo wake daga Arewa zuwa Orlu yana da iyali matansa 2 ‘ya’yan sa 2 shine Wanda Gwamna ya ba da kudi naira dubu 500 biyar suci abinci na mayi magana da iyalan nasa ta waya “. Batun Jihohin su da sunayen su kuwa ya tabbatar da cewa “Ban Sani ba”.

A jihar Ribas kuwa Alhaji musa sa’idu shugaban Yan Arewa mazauna jihar ya tabbatar da wadanda aka kashe mazauna kauyukan Fatakwal ne Bashi da wasu sahihan bayanan su da Kuma Jihohin su na asali ” .

Nima Saida abu ya rinchabe ne aka sanar min an kawo gawarwakin mutanen bani da wani bayani nasu” inji Alhaji sa’idu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here