Ngozi Okonjo-Iwela Ta Zama Shugabar Hukumar Kula da Kasuwanci Ta Duniya

0
144

Ngozi Okonjo-Iwela, yar takara daga Najeriya, ta samu nasarar zama darakta janar na hukumar kula da harkokin kasuwanci ta duniya (WTO).

Okonjo-Iwala ta samu kuri’u 104 daga kasashe 164 mambobin hukumar, inda ta doke abokiyar karawarta daga kasar Koriya ta Kudu.

Hakan ya sa ta kafa tarihi, wacce ta zama yar Afrika ta farko da ta samu wannan matsayi.

Ana saran za’a yi sanarwa a hukumance nan da karfe 3 na rana.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here