Gwamna Matawalle Ya Roƙi Gwamnatin Tarayya Ta Saki Tallafin Biliyan 10 Ga Wadanda Ayyukan Ƴan Bindiga Ya Shafa a Jihar

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya roki gwamnatin tarayya da ta saki kudi Naira Biliyan 10 na tallafi wanda ta yi alkawari tun da fari don tallafawa wadanda barnar yan bindiga da ambaliyar ruwa ya shafa a jihar.

Matawalle, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Bala Bello Maru, ya yi kiran ne a ranar Litinin yayin tattaunawa ta musamman kan al’umaran da ya shafi kasa wamda gwamnatin tarayya ta shirya a Gusau babban birnin Jihar.

Bala Maru, ya ce jihar Zamfara ta na daya daga cikin jihohi na gaba-gaba a arewacin Najeriya wadanda suke fama da matsalar yan bindiga, garkuwa da mutane, satar shanu da matsalar ambaliyar ruwa wacce ta mayar da mutane da dama suka rasa muhallin su, wanda hakan yasa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta saki tallafin na Naira Biliyan 10 don tallafawa wadanda abin ya shafa domin rage musu radadin halin da suke ciki.

Sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gina hanyar Dansadau!Birinin -Gwari zuwa Minna wacce ta ratsa ta jihohin Kaduna Zamfara da Niger a matsayin wani mataki na dakile damar da yan bindiga suke amfani da ita.

Haka kuma ya yi kira da a kafa tsarin aiki tare tsakanin gwamnatin jihar da ma’aikatar jin kai da walwalar jama’a ta hanyar samar da kwamitin hadin gwiwa da zai dinga bayar da talkafi ga al’umma da dama yadda kowa zai amafana.

Ya kuma shaida cewa, jihar Zamfara ba ta fuskanci wani rikici ba a dukkan bangarorin jihar dangane da batun zanga-zangar EndSARS, in da ya yi bayanin cewa, tallafin da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar an raba shi ga wadanda suka chan-chanta a jihar.

Tun da farko, ministar jin kai da walwala jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ce ma’aikatarta ta na ciyar da dalibai 282, 529 karkashin shiyar ciyar da dalibai a gida a jihar Zamfara.

Hajiya Sadiya, ta ce ana aiwatar da shirin ne a makarantu 1, 759 dake kananan hukumomi 14 na jihar.

Ministar ta yi nuni da cewa, kullen da annobar Korona ta haifar, ayyukan yan bindiga da ambaliyar ruwa a yankin arewa maso yamma ya sanya mutane 247, 000 sun rasa muhallan su a jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi, Kaduna da jihar Niger.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here