Za’a Soma Kama Masu Tallar Maganin Gargajiya Ta Hanyar Batsa a Kano

0
114

Sashin Hausa na BBC ya wallafa rahoton cewa, gwamnatin jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya ta kafa wani kwamiti don fara kama masu tallar maungunan gargajiya ta hanyar amfani da kalaman batsa yayin talla.

Kwamitin wanda ke ƙarƙashin kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya ƙunshi jagorancin hukumar Karota da kuma Hisbah, da sauran wasu hukumomin tsaro da masana lafiya.

Ana sa ran jami’an hukumar Karota da na Hisbah ne za su riƙa yin kamen, kafin daga bisani gwamnati ta gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin aikata laifin yin amfani da kalaman batsa, wanda ya saɓa wa doka a jihar.

Babban sakataren cibiyar kula da harkokin lafiya ta jihar Kano Dr Usman Tijjani Aliyu ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai, inda ya ce sun shirya tsaf don fara wannan aiki.

Ya ce ɗabi’ar yin amfani da kalaman da ba su kamata ba a yayin tallata magungunan gargajiya a jihar kuma ta zama ruwan dare, don haka gwamnati ba za ta lamunci ci gaba da yin hakan ba.

Ita dai gwamnatin Kano ta ce ba za ta ci gaba da zura wa masu tallar maganin gargajiya a jihar ido suna abin da ta kira ”Ɓata tarbiyyar al’ummar jihar ba.”

Ruwan dare, gama duniya

Wannan al’amari na tallar magunguna da batsa ya zama ruwan dare gama duniya a arewacin Najeriya, inda kusan ko wacce kasuwa da tasoshin mota da ke jihar Kano ba a rasa masu tallar magungunan gargajiya, kuma yawancinsu kan yi amfani da kalaman batsa wajen yin talla, musamman kan magungunan da suka shafi inganta jima’i.

Wani abu da mutane da dama ke cewa bai dace ba shi ne yadda masu magungunan ke furta irin waɗannan kalamai, ba tare da la’akari da mutanen da ke wajen ba.

”Sai ka taho da ƙanwarka ma, amma su riƙa irin wannan kalamai, yanzu fisabilillahi ya za ka ji? Wannan abin kunya ai ya fi gaban hankali,” in ji Sanusi Zage, wani matashi da ke zaune a ƙwaryar birnin Kano.

Ko da yake a jihohi da dama akwai masu tallar magungunan gargajiya da ke amfani da irin waɗannan kalamai, a iya cewa lamarin ya fi ƙamari a jihar Kano.

Sannan gwamnatin jihar ta sha gargaɗin masu irin wannan sana’a su riƙa tallar cikin ɗa’a, sai dai har yanzu ana ci gaba da samun irin waɗannan al’amura.

Me malamai ke cewa?

Sheikh Hailru Abdullahi Maraya,

”Matan aure sun je kasuwa ko wuraren aiki duk suna ji, yaro tun yana ƙarami yana jin maganganu na batsa wannan zai sa ya tashi da su,” in ji Sheikh Hailru Abdullahi Maraya

Yaya batun yake a mahangar addini?
Sheikh Hailru Abdullahi Maraya, fitaccen malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, ya ce amfani da kalaman da ba su kamata ba a cikin jama’a ya saɓa da tarbiyya, da kuma koyarwar addinin Musulunci.

Ya ce gwamnati na da damar ɗaukar mataki don kiyaye addini da kuma al’adar mutane, don gudun ɓata tarbiyyar jama’a.

”Na farko dai ka ga yawanci ana yi ne a lasifikoki, saboda haka mata da ƙananan yara duk suna ji ƙwarai da gaske”.

”Matan aure sun je kasuwa ko wuraren aiki duk suna ji, yaro tun yana ƙarami yana jin maganganu na batsa wannan zai sa ya tashi da su, don haka ɗaukar mataki a kan irin wadannan abu ne mai muhimmancin gaske,” in ji Sheikh Halliru Abdullahi Maraya.

Sai dai ya buƙaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su fara wayar da kan masu tallar magungunan gargajiyar kafin ɗaukar irin wannan mataki.

Ita dai gwamnatin Kano ta ce ta sha jan hankalin masu magungunan gargajiya a jihar su guji yin irin waɗannan kalamai yayin da suke yin talla, amma hakan bai hana su dainawa ba, sai dai fitaccen malamin ya ce ya danganta da irin jan hankalin da aka yi musu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here