“Na Yafewa masu zargina da Ɓoye Tallafin Korona” – Sadiya Umar Faruoq

0
218

Ministar Jin ƙai da walwalar jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ce ta yafewa wadanda su ka soke ta bisa boye kayan tallafin cutar Korona da za’a rabawa talakawa.

Ta yi bayyana hakanne yayin da take amasa tambayoyin manema labarai a garin Gusau ranar Litinin.

“Ina sane da cewa, mutane da dama sun yi zarge-zarge tare da suka ta da ma’aikata ta bisa yadda muka raba tallafin rage radadin Korona.

“A kodayaushe ina fada, ina gudanar da aikina da sauke nauyin da yake a kaina kamar yadda zan iya tare da adalci ga dukkan bangarorin kasarnan.

” Yanzu sun gane kuskuren su, zan yi addu’a ne kawai Allah ya yafe mu gabadaya”, inji ta.

Kamfanin dillacin labarai na kasa, (NAN), ya rawaito cewa ministar tunda farko ta kai ziyara ga Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, inda Sarkin ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kara duba kan yanayin tsaro a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here