Mun Raba Tallafin Kuɗi Sama Da Biliyan 6 Ga Talakawa Mabukata a Jihar Zamfara – Sadiya Umar Farouq

0
146

Ministar jin ƙai da walwalar jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ce ma’aikatarta ta raba tallafin kuɗi Naira Biliyan 6, 091, 580, 00 ga magidanta talakawa dubu 129, 137 a jihar Zamfara.

Ministar ta yi bayanin hakan ne yayin tattaunawa da Sarakuna da masu ruwa da tsaki a fadar gwamnatin jihar Zamfara, dake Gusau, kamar yadda yake ɗauke a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Adeyemo Felicia ya fitar.

Ministar ta ce an raba kudin ta hanyar tsarin bayar da tallafin kuɗi na gwamnati ga talakawa mabukata da na bayar da tallafin dubu biyar duk wata ga gajiyayyu a jihar.

Ta ce, shirin anyi shi ne don fitar da su daga talauci.

Ministar ta kara da cewa , “Dokar kulle ta annobar COVID-19 ta haifar da matsala ga tattalin arzikin kasa da harkokin yau da kullum”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here