Maulud: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Alhamis A Matsayin Ranar Hutu

0
195

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin bikin tunawa da ranar haihuwa ANNABI MUHAMMAD Tsira da Amincin Allah su Kara tabba a gare shi.

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana sanarwar a madadin gwamnatin tarayya a yau Talata, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mohammed Manga, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar.

Aregbesola Ya bukaci yan Najeriya musamman mabiya addinin musulunci a wannan lokaci, su kaucewa rikici, karya doka kamar yadda ake ganin hakan a yan kwanakin nan.

Ministan, wanda ya bayyana matasa a matsayin nasara ga kasarnan, ya shawarce su da su karfafi tsarin dimukuradiyya,  ba su karya shi ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here