An yi Garkuwa Da Matar Dagacin Garin Tsara a Masarautar Karaye Dake Kano

0
120

Masarautar Karaye ta sanar da cewa wasu yan bindiga sun yi garkuwa da matar dagacin garin Tsara a karamar hukumar Rogo, mai suna Aishatu Aliyu.

Kamar yadda rahotan da Wamban Karaye, Alhaji Muhammad Mahraz ya gabatarwa da Sarkin Karaye, Alhaji Dr. Abubakar Ibrahim II ya bayyana cewa, wasu da ba a san ko su waye ba sun shiga gidan dagacin Tsara da safiyar Ranar juma’a tare da sace matar sa.

Rahotan ya kara da cewa, an samu harsashin da aka yi amfani da shi guda 17 a wajen da lamarin ya faru. Wanda hakan ya sanya mutane da dama dake zaune a kauyen yin kaura zuwa daji don tsira da ransu.

Har kawo lokacin da aka gabatar da rahotan ga Sarkin, ba a samu labarin inda Aishatu Aliyu ta ke ba.

Hakimin ya kuma bayyanawa Sarkin cewa, mutanen Rogo suna cikin fargaba a yayin da ake samun yawaitar yin garkuwa da mutane.

Yayin da yake mayar da martani, Sarkin Karaye, Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II ya kara yin kira ga hukumomin tsaro da su samar da matakan tsaro don kawo karshen dukkan ayyukan bata gari a masarautar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here