Zanga-Zangar EndSARS: Ana Yi Mana Barazana Da Takunkumin Hana Shiga Kasashen Ƙetare – Burutai

0
234

Babban Hafsan sojin kasa, Janar Tukur Buratai, yaki amincewa da kiran da ake yi ga kasashen duniya na su sanya takunkumin hana shiga kasashen su ga wasu manyan jami’an tsaron soji bisa zargin take hakkin wasu yan Najeriya yayin zanga-zangar EndSARS.

Buratai ya bayyana hakan ne a yau Litinin a Abuja yayin taron tattaunawa manyan janar na soji dake kula da shiyoyi kan zanga-zangar EndSARS.

Ya ce: “Masu Aikata laifuka, su na yi mana barazana da hana shiga kasashen ketare amma ran mu baya baci saboda dole ne mu zauna a kasarnan don ciyar da ita gaba.

“Lokaci na farko da na fara fita daga kasarnan, ina dan shekara 50 kuma lokacin ina Janar na soja, don haka bazan damu ba idan na gama rayuwata a nan”.

Buratai ya kara da cewa, Rundunar soji na kokari wajen tabbatar da tsarin dimukuradiyya a Najeriya. Babban tsarin tafikar da gwamnati shi ne na Dimukuradiyya kuma dole ne dukkan mu mu tabbatar da tsarin dimukuradiyya na Najeriya cikin kwanciyar hankali da kuma ci gana” inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here