Zanga-Zangar EndSARS: An Harbi Dan Jarida Da Wasu Mutane Da Dama A Jihar Kogi

0
92

Wakilin Jaridar The Sun a jihar Kogi Emmanuel Adeyemi na daga cikin mutanen da aka harba a garin Lokoja yau Litinin yayin fada tsakanin masu zanga-zanar EndSARS da yan daban siyasa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa(NAN) ya rawaito cewa an harbi Mista Adeyemi ne a kan hanyar sa ta zuwa cibiyar kungiyar yan jaridu dake titin Lugard a Lokoja, yayin da aka harbi wani mutum a dai-dai hanyar.

An ruga da mutanen biyu zuwa karamin asibitin Lokoja inda yanzu haka suke karbar magani.

Yan bindiga sun harbi mutane da dama wadanda suka shiga zanga-zangar.

Haka kuma yan daban wadanda ke tafiya a motoci guda biyar, sun je mahadar titin Cemetery inda suka dinga harbi kan iska.

An rufe shagunguna da kasuwanni ya yin da kowa ke gudun tsira da ransa.

Lamarin ya tilastawa yan jarida a Lokoja buya bayan bayanan da ke bayyana cewa yan bindiga na neman su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here