Gwammatin Jihar Kuros Riba Ta Ware Ladar Naira dubu 100

0
106

Daga Musa Muhammad Kutama a Kalaba

Gwamnan Jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade , ya ware ladar zunzurutun kudi naira dubu 100 lada ga Duk Wani Wanda ya fallasa inda aka boye kayan gwamnati da masu zanga-zangar Endsars da zauna gari banza suka sace suka boye.

 

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai kuma mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai christian Ita ya sanyawa hannu aka rabata ga manema labarai.

Sanarwar tace “an ware ladar naira dubu dari ga Duk Wani Wanda yasan inda aka boye kayan gwamnati da ɓata gari Suka sace.

An shafe tsowon kwanakin Alhamis da juma’a zuwa Asabar masu zanga-zangar Endsars da zauna gari banza suna sace kayan.

Matasan sun kai Hari tare da sace kayan gwamnati wurare sama da 50 a fadin jihar kuros Riba.Lamarin da ya jefa al’ummar jihar kuros riba cikin Wani halin.

Kadan daga cikin wurare da suka afka suka sace kayan gwamnati sun hada da Asibitin Mahaukata suka kuma sauke majinyata kasa Suna sace gadajen kwanciyar su da katifun suna arcewa hatta ma asibitin masu cutar tarin fuka ma sun sace kayan da aka dauki samfurin yawun masu cutar tarin fuka Dana cutar kurona sun tafi tashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here