Shugaban Hukumar Kula da Sadarwa Ta Kasa, NCC Ya Kai Ziyara Ga Sarkin Kano

0
95

Shugaban hukumar kula da sadarwa ta kasa, NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta ya kai ziyara ga mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, inda ya bukaci al’ummar jihar su ci gaba da bada goyan baya ga shirye-shiryen gwamnatin tarayya don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarnan.

Dambatta, wanda dan asalin jihar Kano ne ya yabawa masarautar da al’ummar Kano gabadaya bisa goyan bayan su ga gwamnati, inda ya ce Najeriya ta chanchanci samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa don cimma muradanta na samun ci gaba.

Ya ce gwamnatin tarayya ta zo da shirye-shirye da dama kan samarwa da matasa aikin yi musamman ta hanyar samar da sana’o’in fasahar zamani.

Anasa jawabin, Aminu Ado Bayero, wanda ya godewa shugaban hukumar NCC din tare da tawagar sa bisa ziyarar da suka kawo masa, ya yabawa shugaban Buhari, ministan sadarwa, Dr. Isa Ibrahim Pantami bisa jajircewar su kan fanni yada labarai da sadarwa.

Sarkin ya kuma yi bayanin cewa, za su ci gaba da bada goyan baya ga gwamnatin tarayya kan shirye-shiryen ta, inda ya bukaci shugabanni da su dabbaka zaman lafiya a tsakanin al’umma a kasarnan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here