Kwalejin Ilimi Ta Isa Kaita Dutsin-ma Ta Sanar Da Ranar Komawa Makarantar

0
164

Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita dake Dutsin -Ma a jihar Katsina ta sanar da ranar 26 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta koma harkokin koyo da koyarwa.

a wata sanarwa da jami’in yada labarai na kwalejin, Mukhtar Balangoggo ya fitar ta ce, komawa makarantar na zuwa ne bayan amincewa da sashin ilimi mai zurfi da ma’aikatar lafiya ta jihar ta yi kan matakan da kwalejin ta dauka na hana yaduwar cutar Korona.

Sanarwar ta kara da cewa, jarrabawar zangon karatu na farko za ta fara ne a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba zuwa 27 ga watan Nuwamba, yayin da zangon karatu na biyu zai fara ranar 30 ga watan na Nuwamb.

Sannan Sanarwar ta shawarci dalibai da su bi ka’idojin da aka shimfida don kariya daga cutar Korona, wadanda suka hada da sanya takunkumin rufe hanci da baki kafin shiga kwalejin, wanke hannu da kuma bada tazara.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here