Buɗaɗɗiyar Wasika Zuwa ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya

0
267

Buɗaɗɗiyar Wasika Zuwa ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya.

Sunana Amb Auwal Muhd Danlarabawa Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe na kasa wadda aka fi sani da suna Grassroot Care and Aid Foundation GCAF.

Ina Mai Kira ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari wajen nemawa matasa tallafi Wanda zai anfane su kuma ya ƙara sanyaya zukatan matasan da ƙarfafa musu cewar Gwamnatin tana sane dasu sannan tana son faranta zukatan su a wannan yanayi da ake ciki Wanda aka dauki dogon lokaci Ana zaune a Gida ba Makarantu.

Kiran nawa dai shine Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fito da wani tsari Wanda zai tallafawa daliban dake Karatu a Makarantun gaba da sakandire ta hanyar neman alkalumansu nasu Daga Makarantu da suke karatu ta lambobin rijistar su na Zama dalibai abi kowanne a bashi tallafin da zai taimaka musu a harkokin rayuwar su dama bangaren neman ilmin nasu.

Wannan tallafi zaiyi matukar anfani kuma zai Kara musu soyayyar kasa da Gwamnatin Baki Daya sannan zai Zama wani banagare na ƙara Samar da zaman lafiya a ƙasa a gefe guda kuma zai rage radadin talaucin da aka tsinci Kai a sakamakon cutar Covid 19 data dagula al’amuran daliban da jefa su cikin bacin Rai na kasa cimma nasarar da suka saka a gaba a fannin karatun nasu Akan Lokacin da suke tsammanin kammalawa.

Ina fatan Gwamnatin Tarayyar Najeriya zata duba wannan shawara tawa Dan tallafawa daliban ƙasar Nan a matakin tallafin Covid 19 da zai rage radadin ƙuncin da dalibai ke ciki Dan Kar a cigaba da anfani da wasu Daga ciki Ana Basu wasu Yan kudade Dan su tada mana hargitsi a ƙasa.

Nagode
Allah ya taimaki ƙasar mu Najeriya ya bamu zaman lafiya da cigaban tattaalin ARZIKI.

Amb Auwal Muhd Danlarabawa
Grassroot Care & Aid Foundation
08060257925 Kano, Nigeria.
amdanlarabawa1@gmail.com

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here