Ƙasar Saudiya Ta Sanar Da Ranar 1 Ga Watan Nuwamba Ranar Dawowa Da Ziyarar Umrah Ga Kasashen Waje

0
213

Ma’aikatar dake kula da aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudia Arabia ta tabbatar da ranar 1 ga watan Nuwamba a matsayin ranar dawowa da ziyarar Umrah ga yan kasashen waje.

Dukkanin kasashen da suka chan-chanci a basu damar zuwa ziyarar Umrah din, ma’aikatar za ta sanar da su.

Idan za’a iya tunawa dai, Kasar Saudia Arabia ta dakatar shiga kasar don aikin Umrah ko aikin Hajji sakamakon annobar COVID-19.

Sai dai sannu a hankali kasar na saukaka matakan da ta dauka na dakile yaduwar cutar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here