Zanga-Zangar EndSARS: Mutane Biyar Sun Rasa Ransu A Jihar Cross River

0
95

Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba

A kalla mutum biyar rahotanni suka nuna sun rasa ransu,  jiya Juma’a lokacin da masu zanga-zangar Endsars da zauna gari banza su ka kai wasoson dukiya da kayan abinci da gwamnatin tarayya ta bayar Tallafi domin rage radadin cutar kurona .

Mutum uku sun mutu yayinda aka bankawa ofishin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kuros Riba wato SEMA bayan shakar hayaki da suka yi sauran mutum biyu Kuma Neman su a ka yi ko kasa ko sama.

Safiyar Asabar din nan masu zanga-zangar sun kone gidan mai mallakar gwamnan Jihar Kuros Riba Farfesa Ben Ayade.Basu tsaya nan ba sun koma gidajen sanatoci masu ci yanzu ciki harda gidan sanata Genshom Bassey .

Hakazalika sun kona bankin first Bank reshen 8miles dake Karamar hukumar birnin Kalaba yau Asabar.

Haka Kuma sun kona kantin zamani na matar tsohon gwamnan Jihar Kuros riba sanata Liyel Imoke wato Uwargida Obioma Imoke.

Yanzu haka sun fantsama sauran wurare a birnin Kalaba Suma ci gaba da abinda sukeyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here