Bola Tinubu, tsohon gwaman jihar Legas kuma jagoran jami’iyyar APC na kasa ya musanta zargin cewa ya gudu ya bar kasarnan.
A wani faifan Bidiyo da jami’iyyar APC ta wallafa a shafinta na twitter an hango Tinubu na fadiin cewa:
“Ba inda naje. Ni dan Legas ne. Har yanzu nine Asiwaju na Legas kuma nine dai Jagora”, inji Bola Tinubu.
Wasu dai sun ta yada cewa Bola Tinubu ya bar kasarnan bayan barkewar zanga-zangar EndSARS.