Yadda Ƴan Daba Ke Amfani Da Babur ɗin Adaidaita Sahu Wajen Ƙwacen Waya A Kano

0
216

Mazauna ƙwaryar birnin Kano sun koka kan yawan samun masu kwacen waya a birnin Kano.

Mutane da dama dai wadanda suke fita atisayen motsa jiki a yankin Nassarawa GRA sun bayyana damuwa kan yadda yan daba masu kwacen waya ke zare makami suna kwace a yankin musamman da yamma lokacin atisayen motsa jiki da kuma sanyin safiya.

Wani dan jarida da abun ya faru a kan idon sa ya bada labarin yadda masu kwacen waya ke amfani da babur mai kafa uku wato Adaidaita Sahu musamman da safe wajen kwacewa mutane waya.

“Yau da Sassafe, a hanyata ta zuwa Race course don motsa jiki, wasu yan daba sun kai farmaki tare da kwace wayoyin wani saurayi da wata budurwa a kan titin Lugard bayan sun zare mu su wuka.

“Yan daban da yawan su ya kai su biyar, sun zo ne a kan Adaidaita Sahu inda suka nufi kan masu wayoyin. Yayin da masu wayar suka yi yunkurin guduwa, sai mai tuka babur din ya toshe musu hanya, wanda hakan ya bada dama ga ragowar yan daban wajen yin kwacen.

“Daga nesa na lura da yadda aka farmaki masu wayayoyin na ga wasu matan na gudu don tsira da rayuwar su.

“Matar da ke kusa da wajen ta fada min cewa, ko a makon da ya gabata ma sai da yan daba su ka farmaki wani mutum inda suka yanke shi kuma suka kwace wayar sa duk a yankin.”

Matsalar kullum na kara tabarbarewa a Kano musamman kwaryar cikin birni.

Mazauna yankin dai sun roki hukumomin tsaro da su kawo musu dauki yankin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here